Zan Yi Koyi Da Bill Gates Wajen Taimakon Al’umma-Dangote

44

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya ce haɗuwa da Bill Gates ya canza masa tunani, musamman wajen yin wani abu don haɓaka rayuwar yaran Najeriya a harkar kiwon lafiya a ƙasar nan.

Mista Dangote ya bayyana haka ne a New York ranar Laraba a yayin Taron Ganawa na Goalkeepers na 2019 na Gidauniyar Bill da Melinda.

A cewar Mista Dangote, aikinsa ta hanyar gidauniyarsa ya taimaka wajen saita manufofinsa wajen cimaka a Najeriya.

“Misali, Gwamnatin Tarayya tana da shiri a kan inganta abinci, abinda ke tilasta masu samar da abinci kamar shinkafa, sikari, alkama, taliyar sifageti, taliyar noodles su saka sinadarai a abubuwan da suke samarwa.

“Lokacin da na kafa gidauniyata a 1994, ban taɓa kula da cewa muna da wannan babban ƙalubalen ba a ɓangaren lafiya.

“A zahiri, abu ne mai sa ƙwaƙwalwa tunani, lokacin da muka cimma wannan yarjejeniya da Gidauniyar Bill da Melinda, kuma wannan ya buɗe min idona wajen gane cewa da akwai ƙalubale a ɓangaren lafiyar ba.

“A wancan lokaci, ban samu damar haɗuwa da Bill ba, amma haɗuwa da Bill ya canza ni zuwa wani mutum daban.

“Wannan fa wani ne da ba abinda ya shafe shi da mu a Afrika ko Najeriya, amma ga shi yana saka kuɗinsa da kuma ransa a cikin komai.

“A jajirce yake wajen taimakon al’umma, kuma hakan ya ba ni mamaki sosai, kuma na gane cewa shi mutum ne mai sauƙin kai, kuma ban taɓa sanin Bill zai zama mai sauƙin kai haka ba. Mutum ne mai taushin kalamai, kuma mai kirki.

“Yana da wahala a samu mutane irin Bill a duniyar nan. Addu’ata kaɗai a shekaru kaɗan masu zuwa ita ce, zan yi ƙoƙarin bada wani ɓangaren dukiyata sadaka”, in ji shi.

Haka kuma, wanda ya samar da Gidauniyar Bill da Melinda, Bill Gates ya ce ba don Dangote ba dai bai samu irin dangantakar da ya samu ba Afirka.

Ya yaba wa Dangote bisa aikinsa na taimaka wa yara don kawo ƙarshen rashin ingantaccen abinci ta hanyar inganta abinci.

Ya ce cin abincin da ya ƙunshi dukkan sinadarin yana da muhimmanci saboda rayuwar yaro idan ya wuce shekara biyar ta dogara ne da abincin da yake ci ko take ci.

Mista Gates ya kuma gode wa Dangote bisa yadda ya kasance abokin na gari, da kuma koya masa yadda zai sadu da jama’a, maimakon aika musu saƙon email ya yi zaton su fahimta, su ga matsalar da mafitar da yake gani.

Ya lura da cewa Bill da Melinda sun iya yin aiki a Arewacin Najeriya ne, da taimakon Dangote, wanda a ƙashin kansa ya kira gwamnoni shida don su saurare shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan