Zancen Mayar Da Sarki Sunusi Bichi Ƙanzon Kurege Ne – Gwamnatin Jihar Kano

201

Gwamnatin jihar Kano ta bakin sakataren yada labaranta Abba Anwar, ta musanta zargin da wata kungiya ta ke wa gwamnatin jihar na shirin da ta ke domin mayar da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu zuwa masarautar Bichi.


Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnatin jihar Mal. Abba Anwar ya ce, ”kawai kururuwa kungiyar take yi sannan bayanan da ta yi, ba su da tushe balle makama.


Tun da farko dai wata kungiya mai zaman kanta da ake kira ‘The Renaissance Coalition’ ta yi zargin cewa, yanzu haka gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin mayar da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu zuwa masarautar Bichi.


Sanarwar da kungiyar ta raba wa manema labarai dauke da sanya hannun Ibrahim A. Waiya, ta bayyana cewar da zaran Sarki Sanusi ya ki amincewa da sauyin da za a yi masa, gwamnatin za ta tube shi daga karagar mulki.


Kungiyar ta bayyana takaici kan shirin wanda ta ce, yana zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka shari’a a kotu kan kalubalantar sabbin masarautu guda 4 da gwamnatin ta kirkiro domin yi wa Masarautar Kano kishiya.


Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da masu karfin fada aji, da su gaggauta tsoma baki wajen janyo hankalin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje wajen kauce wa abin da zai haifar da tashin hankali a jihar baki daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan