An Hana Lauyoyin Sowore Shiga Ofishin SSS

184

A ranar Juma’a ne Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, SSS, ta hana lauyoyin Omoyele Sowore, mawallafin jaridar nan ta Intanet, Sahara Reporters da ake ci gaba da tsarewa shiga ofishinta na Abuja.

Lauyoyin, waɗanda ke wakiltar ɗan gwagwarmayar a Babbar Kotun Tarayya bisa laifuka da suka haɗa da cin amanar ƙasa da almundahanar kuɗi, sun je hukumar ne don su ƙara gabatar da takardun dake nuna cewa ya cika sharuɗdan beli.

A ranar 24 ga Satumba ne Babbar Kotun Tarayyar ta ba Mista Sowore beli bayan ya shafe fiye da kwana 50 a tsare.

Wani lauya daga cikin lauyoyin daFalana ke jagoranta, Samuel Ogala, ya faɗa wa jaridar PREMIUM TIMES ranar Juma’a cewa suna isa ƙofar ofishin SSS ɗin ne sai aka tsayar da su duk da wakilin doka da suke tare da shi a karo na biyu.

Amma jami’an hukumar dake bakin ƙofar ofishin sun karɓi takardun.

Biyo bayan wata sanarwa da mai magana da yawun SSS, Peter Afunaya ya fitar ranar Alhamis cewa har yanzu hukumar ba ta karɓi takardun ba, sai lauyoyin Mista Sowore, waɗanda Mista Falana ke jagoranta suka shirya sabbin takardun hujjoji don gabatarwa ranar Juma’a. Sun ce sun gabatar da irin waɗannan takardun ranar Laraba.

Wani lauya daga cikin lauyoyin da Mata Falana ke jagoranta wanda ya gabatar da takardun neman yi wa umarnin kotu biyayya, Marshal Abubakar ya ce an buƙaci wakilin kotun, wanda aka ɗora wa nauyin gabatar da takardun kotun ya dawo da ƙarfe 12:00 na rana Juma’a bayan ziyararsa ta farko zuwa hukumar ranar Juma’a.

Amma a wata tattaunawa ta waya, Mista Ogala ya faɗa wa PREMIUM TIMES cewa an tare su a bakin ƙofa bayan sun je da ƙarfe 12:00 na rana da wakilin doka.

Lokacin da PREMIUM TIMES ta tuntuɓi mai magana da yawun SSS, Peter Afunaya don ya yi sharhi bisa wannan batu, sai ya ce ba ya ofis a lokacin.

A ranar Talata ne wata Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin a saki Mista Sowore daga hannun SSS.

Amma har yanzu hukumar ba ta yi biyayya ga umarnin ba, sa’o’i 72 bayan an yanke hukuncin.

A wani kiran wayar da PREMIUM TIMES ta yi masa, Mista Ogala ya ce jami’an na SSS sun karɓi takardun daga wurinsu a bakin ƙofa.

Ya ƙara da cewa suna jira ne a bakin ƙofa don ganin shaidar rasiti.

A wani kiran wayar da PREMIUM TIMES ta yi, Mista Ogala ya ce jami’an na SSS ba su karɓi takardun daga wajensu ba a bakin ƙofa.

_Rubutun Edita: An sabunta wannan rahoto don a nuna cewa SSS sun ƙi karɓar takardu dake nuna lallai a yi biyayya ga sharuɗɗan belin Mista Sowore.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan