Ko Me Yasa Buhari Ya Dawo Daga Amurka Kafin Ranar Da Ya Kamata Ya Dawo

169

A ranar Asabar da safe ne Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Babban Birnin Tarayya, Abuja bayan ya halarci Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Karo na 74, UNGA74 a birnin New York na Amurka.
Shugaban dai ya dawo kwana ɗaya kafin ranar da ya kamata ya dawo.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, tun farko an tsara Shugaban zai dawo ne a gobe Lahadi da misalin ƙarfe 7:00 na safe.

To, amma, jirgin da yake ɗauke da Shugaban Ƙasar, hadimansa da wasu ‘yan tawagarsa ya sauka a Sashin Saukar Jirgin Shugaban Ƙasa na Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikwe dake Abuja ranar Asabar da sassafe.

NAN ya bada rahoton cewa matakin Shugaban na dawowa gida ya biyo bayan iya kammala dukkan abubuwan da zai yi ne a kan lokaci.

Shugaban, wanda ya bar Abuja ranar 22 ga Satumba zuwa New York, ya halarci Manya da Ƙananan Tarukan UNGA74.

Jawabin Shugaba Buhari a hukumance a UNGA74 ya zo ne ranar Litinin inda ya yi wa Taron Ƙolin Majalisar Ɗinkin Duniya na Ɗaukar Mataki Kan Sauyin Yanayi mai taken: “Wani Tsere Da Za Mu Iya Ci. Wani Tsere Da Ya Zama Dole Mu Ci”.

A wajen wannan taron, Shugaba Buhari ya sanar da shirye-shiryen gwamnatisa na canza mummunan tasirin sauyin yanayi a Najeriya.

Yayinda yake musayar ra’ayi bisa abinda Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa duniya na ci gaba da faɗawa cikin annobar sauyin yanayi, Shugaba Buhari ya ce: “Babu shakka, Sauyin Yanayi abu ne da ɗan Adam ke haifarwa”.

A ranar 24 ga Satumba ne ya gabatar da Jawabin Najeriya a matsayin mai jawabi na biyar a ranar farko ta Babbar Muhawarar a yayin UNGA74 inda a cikin sauran batutuwa, ya ankarar da duniya irin yunƙurin da ƙungiyoyin masu aikata laifi na ƙasa da ƙasa ke yi na cutar da Najeriya biliyoyin Naira.

Yayinda yake a UNGA74, Shugaban ya kuma halarci manyan taruka a kan “Tsaftace Ruwa da Haɗe Muradun Ƙarni- Cike Manufar Shiri Don Cimma Muradun Ƙarni Masu Ɗorewa”.

A ranar 26 ga Satumba, Shugaban ya yi jawabi a Babban Taron Gefe na Ƙasa da Hukumar Bunƙasa Haɗin Kan Nahiyar Afirka da Sabon Ƙawancen Ci Gaban Afirka, AUDA-NEPAD suka shirya.

Shugaba Buhari ya kuma yi ganawa daban-daban da shugabannin ƙasashen duniya, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, manyan ‘yan kasuwar duniya da Ƙungiyar Yaƙi da Sauyin Yanayi ta Matasan Najeriya kafin ya bar New York ranar Juma’a.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan