Wasan Hamayya Na Birnin Madrid Ayau

263

Ayau za a buga wasan hamayya na birnin Madrid tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Athletico Madrid inda Athletico zasu karbi bakuncin Real Madrid.

Kungiyoyin kwallon kafan dai dukkansu a birni daya suke kuma akwai hamayya mai karfi a tsakaninsu.

Gabar ta dakko asali ne dai ganin masu hannu da shuni sune sukafi goyon bayan Real Madrid inda masu karamin karfi yawancinsu a Athletico Madrid suke a wancan lokacin.

Gabar ma ta sake tsami a ‘yan shekarun baya bayan da Real Madrid ta lallasa Athletico Madrid a wasannin karshe guda 2 na gasar zakarun nahiyar turai.

Haka na a wasannin share fage a kwanannan Athletico Madrid ta casa Real Madrid daci 7 da 3.

A yau da misalin karfe 8:00 na dare agogon Najeriya Athletico Madrid zasu karbi bakuncin Real Madrid awasan mako na 7.

Real Madrid dai har yanzu basuyi rashin nasara ba a gasar ta Laliga inda suka lashe wasanni 4 suka buga kunnen doki guda 2 inda suke jan ragamar teburin gasar da maki 14.

Athletico Madrid ne a matsayi na 2 da maki 13 inda sukayi rashin nasara a wasa 1 suka buga kunnen doki guda 1.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan