Al Hilal Sun Lashe Enyimba Agasar Zakaru

179

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba tayi rashin nasara a wasan da suka fafata da Al Hilal ta kasar Sudan a yammacin yau Lahadi.

Al Hilal din sun lashe Enyimba daci 1 da nema awasan zagaye na biyu.

Awasan farko anan gida Najeriya kungiyoyin kwallon kafan guda biyu sun tashi kunnen doki wato babu ci a tsakaninsu.

Ayanzu dai ta tabbata cewa Enyimba sunyi waje a gasar zakarun nahiyar ta Afrika inda yanzu babu wata kungiyar kwallon kafa daga Najeriya datake wakiltar Najeriya tunda an fitar da Kano Pillars tun a farko yanzu ma Enyimba sun fita.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan