Ban San Komai Ba Game Da DADIYATA – Nadiya Ahmad

194

Wani rahoto da jaridar Mikiya ta wallafa a shafinta na Facebook mai ɗauke da bayanin ikirarin wata matashiya mai suna Pharydah Faysal Whazeery akan tana da masaniyar in da DADIYATA ya ke, akwai kuskuren hoto a jiki.


Tun da farko an saka hoton wata Matashiya ce mai suna NADIYA AHMAD, a maimakon hoton Pharydah Faysal Whazeery wacce ta ke ikirarin hakan!


Nadiya ta bayyana wakilinmu cewa
“Na samu kiran waya daga sassa daban-daban na ƙasar nan, akan cewa an ga hoto na tare da wani labarin ina da masaniyar in da DADIYATA ya ke, gaskiya bani da alaƙa da labarin kuma domin ba ni ce na wallafa shi ba” in ji Nadiya


A ƙarshe ta buƙaci da mutane da su yi watsi da wannan labari mai ɗauke da hoton ta, domin ba shi da tushe balle makama.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan