Kotun Kano Ta Sa Ranar Yanke Hukunci A Ƙarar Abba Da Ganduje

184

Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Kano ta sa Laraba, 2 ga Oktoba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Abba Kabir Yusuf suka shigar gabanta, inda suke ƙalubalantar bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na ranar 9 ga Maris, 2019.

Sakataren Kotun ne ya sanar da wannan rana a rubutaccen saƙon waya da ya tura wa masu ƙara da waɗanda ake ƙara.

A ranar 18 ga Satumba, waɗanda ake ƙara, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje- sun gabatar da rubutaccen jawabinsu na ƙarshe, kuma masu ƙara su ma, Abba Kabir Yusuf da PDP sun bayar da nasu rubutaccen jawabin.

Shugabar Kotun, Halima Shamaki, ta ce gungun alƙalan kotun suna sane da wa’adin kwanaki 180 da Dokar Zaɓe ta tanada, hakan shi yasa ta kammala aikinta, take kuma son yanke hukunci a cikin da doka ta tanada.

A muhawararsu a lokacin gabatar da jawaban ƙarshe, dukkan lauyoyin waɗanda ake ƙara, Ofiong Ofiong, SAN, Alex Ezinyon da Ahmed Raji SAN sun amince gaba ɗaya da cewa kotun ta yi watsi da ƙarar saboda masu ƙara ba su iya gabatar da hujjoji ba.

Amma da yake mayar da martani, lauyan PDP da ɗan takararta, Kanu Agabi, SAN, ya kawo wuta hujja daga jawabin INEC na ƙarshe cewa Hukumar Zaɓen ta tabbatar da iƙirarin masu ƙara cewa ta gudanar da zaɓe na adalci kuma tsaftatacce a ranar 9 ga Maris, 2019.

Mista Agabi ya jaddada cewa INEC ta yadda a jawabinta na ƙarshe cewa PDP da ɗan takararta suna gaba da halattatun ƙuri’u, kuma an tattara sakamako, an sanar.

A cewarsa, bayan nan ne sai INEC ta yanke shawarar soke mazaɓu 207 wanda ya saɓa da doka.

“INEC ta sanar da sakamakon zaɓen 9 ga Maris, to mu a wajenmu, wannan abu ne mai sauƙi sosai, abinda muke buƙata kawai daga wannan kotu mai alfarma shi ne ta bayyana wanda ya lashe zaɓe bisa halattatun ƙuri’u, wanda shi ne ɗan takarar PDP, Abba K Yusuf, kamar yadda yake a hujjarmu ta ɗaya, tabbataccen kwafin sakamakon zaɓen jiha da INEC ta bayar da kanta”, in ji shi.

To, amma lauyan Ganduje, Ofiong Ofiong, ya ce idan PDP tana so ta yi iƙirarin lashe zaɓen 9 ga Maris, dole jam’iyyar ta gabatar da dukkan sakamakon zaɓen mazaɓun jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan