Yadda Sarki Sanusi Ya Naɗa Sarkin Hausawan Ƙasashen Turai A Paris

56

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya naɗa Dakta Surajo Jankado Labbo a matsayin Sarkin Hausawan Ƙasashen Turai a wani ƙayataccen biki da aka yi a Paris a ƙarshen mako.

Wannan dai shi ne zaman fada na farko da Sarkin ya yi a Turai, inda aka sa masa wata kujera ta ƙawa, aka kuma ɗauki hotunan al’ummomi garin a matsayin dogarai.

A yanzu dai Mista Labbo ya zama Jagoran Al’ummar Hausawa a Turai.

Magajin Garin Palaiseau, Gregoire de Lasteyrie yana ɗaya daga cikin manyan baƙin da suka halarci bikin naɗin.

Sarkin ya je Turai ne bayan ya halarci Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Karo na 74 a New York.

Ana girmama Sarkin Kano a duk duniya, duk da yana fuskantar ƙalubale a gida da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan