Yau Jagoran Zanga-Zangar Juyin Hali Zai Gurfana Gaban Kotu

172

Yau litinin ake sa ran gurfanar da Omoyele Sowore gaban kotu, tsohon dan takarar shugabancin ƙasar nan a jami’iyyar AAC, kuma jagoran zanga-zangar juyin juya hali ta ‘RevolutionNow’ da ba ta yi nasara ba.


Tun da farkon dai Sowore dake tsare a hannun hukumar tsaro ta DSS, na fuskantar tuhume-tuhumen da suka hada da cin amanar kasa, da kuma almundahanar kudade.


Kwanaki shida da suka gabata kotu ta bada umarnin sakin Sowore bayan cika ka’idojin Beli a ranar 25 ga Satumban da muke, amma hukumar DSS ke ci gaba da tsare shi, saboda sabbin tuhume-tuhumen data bijiro da su akansa.


Idan za’a iya tunawa dai a cikin watan Agustan da ya gabata, babbar kotun ƙasar nan ta bada izinin tsare jagoran zanga-zangar ta RevolutionNow amma tsawon kwanaki 45.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan