Ankara Fadada Kwamitin Shirya Gasar Dr Ahlan Pre Season

154

Kasa da mako guda ne yarage a fara gasar share fage mai taken Ahlan Pre season karo na uku.

Shugaban gasar wato Dr Sharu Rabiu Inuwa Ahlan shugaban hukumar kwallon kafa ta jahar Kano kuma wakili a hukumar kwallon kafa ta kasa ya bayyanawa jaridun yanar gizo na Labarai24 da Wasa.ng cewar an kara fadada kwamitin gasar.

Dr. Ahlan ya bayyana cewar ‘yan kwamitin tsare tsaren gasar akwai Isec Danladi da Mataimakinsa wato Auwal Baba Jade, sannan akwai General Coordinator Jude daga Enyimba, sannan daga cikin fadada kwamitin da akayi anshiga da babban naga takarda a hukumar shirya league ta kasa shima anshigo dashi.

Sannan akwai babban sakatare a hukumar kwallon kafa ta jahar Kano hakazalika akwai Suleman wanda shine sakataren shirya wannan gasa ta share fage wato Ahlan Pre Season.

Ahlan ya kara da cewa akwai Lurwanu Idris Malikawa Garu shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta jahar Kano shine mataimaki na 3, akwai Habibu Audu Fagge da sauran masu ruwa da tsaki aharkar wasanni.

Haka akwai Bord Members na Ahlan guda biyu wato Halliru Sumaila da Hassan Garo, sannan Dr. Ahlan ya kara da cewa za a buda kowa ya shigo ciki domin bayar da gudu mawarsa domin harka ce ta Kano.

Haka an bayyana cewar kungiyoyin kwallon kafa 16 ne zasu fafata wannan gasa inda za a buga wasannin a filayen wasannin Sani Abacha da filin wasan Kano Pillars na sabon gari kai harma da filin wasan Dawakin Kudu.

Za a fara wannan gasa a ranar 6 zuwa 15 ga watan Oktoba wato kwanaki 9 kenan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan