Kwanaki 5 Ne Sukarage Afara Gasar Share Fage Ta Dr Ahlan

218

Kwanaki biyar ne suka rage afara gasar share fage ta Ahalan gasar da akayiwa lakabi da Ahlan Free Season.

Wannan gasa daza a gudanar itace karo na uku kenan acewar shugaban wannan gasa wato Dr. Sharu Rabiu Inuwa Ahlan shugaban hukumar kwallon kafa ta jahar Kano kuma wakili a hukumar kwallon kafa ta kasa.

Ahlan ya kara da cewa dukkanin shirye shiryen sunyi nisa domin kuwa committee na shirya wannan gasa sunyi zama dashi har sau biyu wanda daya zamanma a Abuja sukayi.

Ahlan ya bayyanawa kafafan yada Labaran yanar gizo na Wasa.ng da Labarai 24 cewar ita wannan gasa anayintane kusa da fara league domin kowacce kungiyar kwallon kafa daga cikin kungiyoyin da aka gayyato sugane kusakurensu.

Ahlan yayi misali dangane da Kano Pillars inda yace “A ganina kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars wannan wasan share fage yanada matukar muhimmanci a tare dasu ganin zasuyi gogayya da kungiyoyin kwallon kafa kuma musamman da itace kungiya 1 tilo datake wakiltar jahar Kano a gasar Premier, kuma gasar zata baiwa kungiyar Kano Pillars damar ta fahimci irin shirin da takwarorinsu sukayi saisu daidautasu da nasu shin akwai banbanci? ko akwai ci gaba? wanda a karshen gasar da kungiyoyin zasu fafata masu kallo da masu fashin baki zasu yanke hukunci na gane kungiyoyin da zasu iya da wadanda bazasu iyaba”

Shugaban hukumar kwallon kafan ta Kano baitsaya iya nan ba inda yace masu kallo suzamo masu da’a da wayewa irin ta wasanni na zamani domin baiwa Kano gudun mawa domin Kano sunyi nisa a harkar wasanni yanzu don kuwa Kano suma uwace a harkar kwallon kafa a Najeriya.

Kungiyoyin kwallon kafa 16 ne zasu fafata wannan wasan share fage inda daga cikinsu akwai Kano Pillars da Enyimba da Abia Warriors da Adamawa United da Plateau United da Nasarawa United da Yobe da Jigawa Golden Stars da Niger Tornadoes da Rivers da Kwara da Mountain Of Fire Ministry da da kuma Lobi Stars da sauransu inda Ahlan yace dukkanin kungiyoyin sun tabbatar da cewa zasu halarci wannan gasa.

A gasannin baya guda 2 da aka kammala na 2017 da 2018 duka kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ce ta zamo zakara inda ta doke kungiyoyin kwallon kafan Akwa United da Wikki Tourist a wasannin karshe.

Za a fara wannan gasa ta Ahalan Free Season karo na 3 a ranar 6 ga wata a karkare ranar 16 ga watan 10, 2019.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan