Babbar Yaya: Najeriyarmu A Yau

Ina taya ƙasata Najeriya murnar samun ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya. Duk da ina sane sarai har yanzu Najeriya tana cikin shekarun ƙuruciya domin kuwa har yanzu, shekara 59 take, ba ta ƙarasa shekarun manyantaka ba, ma’ana shekara 60. Duk da haka ba zan rasa ɗan abinda zan tofa ba ko da a ce ba shi da yawa. Na kalli ƙasashen da suke sa’anninmu da waɗanda suke ƙannenmu da yayyanmu da muka samu ‘yancin kai tare, sai san barka. Sai na tuna wani littafi da na taɓa karantawa haka yasa na ga cewa ya kamata mu kalli me ake kira ‘ci gaba’ (Development), domin gane mene ne ainihin tambayar da za mu yi wa kanmu.

Zai fi kyau in ɗora bayanina kan mahangar masanin nan, Dudley Seers domin fahimtar matakin da Najeriya ke ciki. Dudley, ya ce, kafin a ambaci ƙasa a matsayin wadda ta samu ci gaba, dole ne sai an samar da amsa ga waɗannan tambayoyin:

  1. Me ke faruwa da talauci?
  2. Me ke faruwa da rashin aikinyi?
  3. Me ke faruwa ga bambanci tsakanin mata da maza?

Idan waɗannan abubuwan guda uku suka yi ƙaranci a cikin al’umma, a kan kira wannan al’umma da wadda ta samu ci gaba. Amma idan aka samu yawaitar waɗannan abubuwa guda uku a cikin al’umma, a kan kira wannan al’umma da wadda ba ta ci gaba ba. Kodayake a wani zancen, masani Dudley ya bayyana cewa, ba wai sai dukkan ukun sun yi ƙamari ba ne sannan za a ce al’umma ba ta ci gaba ba, duk lokacin da aka samu guda ɗaya daga cikin ukun ya ta’azzara, babu makawa wannan al’umma ba ta ci gaba ba.

Idan muka kalli Najeriyarmu da kyau, sai dai mu haɗiyi yawu, mu yi ajiyar zuciya idan aka zo maganar talauci. Ƙididdigar masana ta tabbatar da cewa kashi 85% na mutanen Najeriya na rayuwa ne cikin matsanancin talauci. Wannan kashi 85% na al’umma su ne mutanen da Dalar Amurka ɗaya ta fi ƙarfinsu a rana.

Ba wai kawai matasa ba su da aikin yi ba ne wannan matsanancin talauci ya dabaibaye ba, ta yadda Dalar Amurka ɗaya ta fi ƙarfinsu a rana, wannan hatta a tsakankanin magidanta, waɗanda ke da iyalai. Mutumin da Dalar Amurka ɗaya ta fi karfinsa a rana, wane irin talauci ka ke tsammani yake ciki? Ta yaya za a yi ya iya ciyar da iyalinsa, ballantana a yi maganar tufafi da karatunsu?

Bambancin da ake nunawa a tsakanin maza da mata wani abu ne wanda ke matuƙar addabar mu. Wannan shi ma a fili yake. Mahaifi ya fi ganin muhimmancin ‘ya’yansa maza fiye da mata, saboda yana ganin ai ko ba komai, idan mace ta ɗan tasa, aure za ta yi ta koma ƙarƙashin ikon wani. Wannan bahagon tunanin ne yasa ba a muhimmantar da karatun mata, yawancinsu daga firamare sun kammala kenan sai kuma aure, wasu kuma kaɗan su kan yi sakandare, shike nan, ‘yan ƙalilan ke samun damar zuwa jami’o’i. Haka kuma a wuraren aiki, an fi muhimmanta yi wa maza ƙarin girma da bayar da muƙamai masu muhimmanci fiye da mata. Saboda har yanzu a Najeriya ana ganin cewa tunani da ƙwaƙwalwar mace ba ɗaya ba ne da ta namiji. Wanda wannan sam ba haka ba ne, wasu matan ma sun fi maza tunani da kaifin basira sau dubu.

Batun rashin aikin yi kuwa a Najeriya sai dai a shafa Fatiha. Saboda ba ma kawai wai ana zancen waɗanda ba su da aiki ba ne, a’a, ana batun ma’aikatan dake rasa ayyukansu alhali ga wasu miliyoyi nan a waje, waɗanda ke zaman jiran tsammanin samun aiki. Lamarin rashin aiki a Najeriya na da alaƙa da cin hanci, zalunci da danniya. Mutum ɗaya zai sace dukiyar da za a iya ciyar da ƙananan hukumomi, mutum ɗaya zai sace dukiyar ma’aikata. Waɗannan na daga cikin dalilan da suka sa har yanzu ba mu ci gaba ba, kuma matuƙar aka ci gaba da tafiya a haka, to babu ranar samun ci gaba a Najeriya.

Daga
Shuaibu Lawan,
shuaibu37@gmail.com
October 01-2019

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan