Dalilan Da Suka Sa Abba Bai Yi Nasara Ba A Kotu

214

Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Kano ta tabbatar da nasarar gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje.

Shugabar Kotun, Halima Shamaki ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir Yusuf suka shigar gabanta inda suke ƙalubalantar nasarar Gwamna Ganduje.

Mai Shari’a Shamaki ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta yi dai-dai da ta bayyana zaɓen 9 ga Maris a matsayin wanda bai kammala ba, haka kuma ta yi dai-dai da ta bayyana Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaɓe zagaye na biyu.

Bayan yanke hukuncin, Mai Shari’a Shamaki ta buƙaci waɗanda hukuncin bai yi wa daɗi ba su zauna lafiya, su kuma ɗauka ƙara zuwa kotun gaba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan