Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Malam Muhammad Garba, ya roƙi jam’iyyar PDP da kar ta ɓata lokacinta da kuɗaɗenta wajen ɗaukaka ƙarar da ba su yi nasara ba ƙarara.
Labarai24 ta kawo rahoton cewa a yau Laraba ne Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Kano ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir Yusuf suka shigar gabanta inda suke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ya samu.
Mista Garba ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yayin da yake mayar da martani ga hukuncin da kotun ta yanke ranar Laraba a Kano.
Sanarwar ta ce ya kamata PDP ta karɓi faɗuwa cikin mutunci, ta kuma yi watsi da yunƙurin ɗaukaka ƙara game da hukuncin da Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Kano ta yanke, wadda ta yi watsi da ƙarar.
Ya ce sakamakon nazartar zaman kotun, PDP ta kasa kafa hujjar cin zaɓe, an kuma yi watsi da ƙarar saboda rashin hujja.
Mista Garba ya lura da cewa PDP da ɗan takararta ba su da dalilin ɗaukaka ƙara game da hukuncin, kuma ta nuna dattaku ta kuma guji zafafa siyasa, ya ce PDP ta yi wa mutane ƙarya cewa an yi mata maguɗi ne.
Tsohon Kwamishinan ya roƙi al’ummar Jihar Kano musamman ‘yan jam’iyyar APC da magoya baya da su ci gaba da zama lafiya, su kuma guji tayar da hankali, saboda jami’an tsaro ba za su bari a karya doka da oda ba a jihar.