Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Tambuwal

131

Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Sakkwato ta tabbatar da nasarar Gwamna Aminu Tambuwal na jihar.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da Ahmed Aliyu, ɗan takarar jam’iyyar APC, wanda ke ƙalubalantar nasarar Gwamna Tambuwal.
Tambuwal, wanda ya yi takara ƙarƙashin jam’iyyar PDP bai yi nasara ba a zaɓen farko da aka gudanar ranar 9 ga Maris, 2019.

Kotun ta ce Mista Aliyu ya kasa kafa hujjar dake nuna cewa an saɓa ƙa’idoji a zaɓen.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan