Nasarar Gwamna Ganduje Nasarar Al’ummar Jihar Kano Ce – Kwamared Mai Kasuwa Rano

130

Tsohon Shugaban ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Kano Kwamared Ali Mai Kasuwa Rano ya bayyana nasarar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a matsayin nasarar al’ummar jihar Kano gaba ki ɗaya.


Kwamared Mai Kasuwa ya bayyana hakan ne jim kaɗan da yin fatali da ƙarar da Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya shigar akan nasarar da Gwamna Ganduje ya yi


“Haƙiƙa nasarar da Gwamna Ganduje ya yi nasara ce ga al’ummar Kano gabaki ɗaya, musamman idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin khadimul islam ta ke yin aiyukan da za su inganta rayuwar al’ummar jihar Kano” in ji Mai Kasuwa


A ƙarshe ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar jihar Kano da su baiwa gwamnatin Ganduje goyon baya domin kai jihar Kano gaba.


Idan za’a iya tunawa dai a yaune kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi watsi da ƙorafin da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gabatar a gabanta akan nasarar da gwamna Ganduje ya yi a zaɓen shekarar 2019

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan