Acigaba da kokarin da Xavi yakeyi amatsayinsa na mai horas wa acikin kungiyoyin kwallon kafan dake kasar Qatar ya lashe kyautar gwarzon mai horas wa na watanni biyu wato watan Augusta dana Satumba.
Amma ya lashe ne a gasarsu ta league da suke bugawa mai taken Qatar Stars League.

Ga dalilan dasuka sa ya lashe kamar haka:
Ya jagoranci kungiyarsa a wasanni 4 inda ya lashe wasannin duka kuma yasami maki 12.
Daga cikin wasannin 4 dai daya lashe kungiyar tasa ta jefa kwallaye 16 inda aka jefa musu kwallaye guda 4.
Turawa Abokai