Sakamkon gyare gyare da rundunar yan sanda ta aiwatar a dakunan ajiye masu laifuka a chaji ofis dake Kano da kewaye, rundunar ta ce tana maraba da masu sha’awar shiga domin yada zango ko shakatawa.
Kakakin rundunar yan sanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna ke bayyana haka cikin shirin yansanda da jama’a na gidan rediyon Dala fm, wanda ake watsawa ranakun Talata da rana.
DSP Haruna yace wannan bangare ne na gyare gyare da rundunar ta sanya gaba domin kyautatawa rayuwar wadanda ke jiran shari’a ko kuma yada zango na dan lokaci yayin tuhuma.
Rundunnar ta kuma roki al’ummar dake sabbin unguwanni su hada kai da rundunar domin kawar da manyan laifuka da ka iya afkuwa a unguwannin nasu.
Shirin na wannan rana ya karbi bakuncin sashen bincikar manyan laifuka wato SARS, domin amsa tambayoyi akan irin ayyukan da suke aiwatar wa.
Rahoton Dala FM