Wakilin PDP Ne Ya Ƙwace Sakamakon Zaɓen Gama- Kotun Kano

195

Ba kamar yadda mutane da yawa suka ƙudurce ba, a ranar Laraba ne Shugabar Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Gwamna ta Jihar Kano, Mai Shari’a Halima Shamaki ta bayyana abinda ya girgiza mutane game da zaɓen mazaɓar Gama da aka yi ta ce-ce-ku-ce a kai.

Idan dai za a iya tunawa, a tsakar daren 11 ga Maris ne, bayan kammala zaɓen gwamna a Jihar Kano, jami’an ‘yan sanda suka kama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sulen Garo bisa zargin su da yaga sakamakon zaɓen Mazaɓar Gama.

A wancan lokaci, mutanen biyu sun yi dirar mikiya a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Nasarawa da misalin ƙarfe 3:00 na dare a cikin motoci ƙirar SUV guda uku, daga nan suka wuce Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Jiha inda suka yaga takardun sakamakon zaɓen Ƙaramar Hukumar Nasarawa.

Amma, lokacin da take gabatar da hukunci ranar Laraba game da zaɓen gwamna, Mai Shari’a Shamaki ta bayyana cewa wani wakilin PDP, Umar Tanko Yakasai ne ya yaga sakamakon zaɓen Mazaɓar Gama mai cike da rikici.

A hukuncin nata, Mai Shari’a Shamaki ta zargi Mista Yakasai da kulle kansa da gangan don samun damar sauya sakamakon.

Wannan hukunci ya wanke Mista Gawuna da Mista Garo a fili waɗanda aka kama su da hannu dumu-dumu yayinda suke yaga sakamakon zaɓen Mazaɓar Gama a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Nasarawa.

“Shaidun baƙaƙen takardu da masu ƙara suka gabatar mafiya yawa ba sa ɗauke da hatimi, wasu ba sa hannu. Wasu kuma suna ɗauke da bayanan da aka sake rubutawa, saboda haka, wannan takardu ne masu ƙunshe da jita-jita, kuma ba za a karɓe su ba.

“Kulle kai da Dakta Yakasai ya yi, ya ba shi damar sauya sakamakon zaɓen da ya ƙwace”, in ji ta.

Labarai24 ta ruwaito cewa a ranar Laraba ne kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna Abba Kabir Yusuf suka shigar gabanta inda suke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaɓen 23 ga Maris, saboda rashin hujja.

Haka kuma, Mai Shari’a Shamaki ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta yi dai-dai da ta ayyana zaɓen gwamna na 9 ga Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan