‘Yan wasan Najeriya wato Golden Eaglets zasu kafa sansanin daukan horo a birnin kasar Brazil wato Sai Paulo.
Zasu kafa sansanin horonne a karkashin jagorancin mai horas wa wato Manu Garba inda zasuyi hakanne domin sabawa da yanayin kasar Brazil inda Brazil dinne zasu karbi bakuncin gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekara 17.

Najeriya dai sun lashe gasar sau 5 ta cin kofin duniya a tarihi.
Za a fara gasar ta cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekara 17 a watan Nuwamba na 2019 a kasar ta Brazil.

Turawa Abokai