Zan Ƙalubalanci Gwamna Ganduje A Kotun Kaduna – Abba Gida-Gida

171

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano, ya ce sun daukaka ƙara domin ƙalubalantar tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi.

Abba Kabir Yusuf ya shaida wa BBC cewa tuni lauyoyinsu suka cike dukkanin takardun da ake buƙata na ɗaukaka ƙara.

“Mun shigar da ƙara domin kare hakkin al’ummar jihar Kano,” in ji shi.

Mai shari’a Halima Shamaki ce ta yi watsi da karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar a ranar Laraba inda ta tabbatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.

Mai shari’a Shamaki ta yi watsi da karar da dan takarar na jam’iyyar PDP ya shigar ne bisa gaza gamsar da kotun cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris.

Sai dai jam’iyyar PDP na da ‘yancin daukaka kara har zuwa kotun koli, idan har hukuncin bai musu dadi ba.

Dan takarar na jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya ce sun tanadi manyan lauyoyi guda bakwai da kanana sama da 40 da za su kalubalanci hukuncin. “Muna da yakinin za mu yi nasara,” in ji shi.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan