Wani kunkuru mai shekara 344 a duniya da aka fi sani da Alagba, a Fadar Soun na Ogbomosho dake Jihar Oyo ya mutu.
Kunkurun ya yi rashin lafiya na wasu ‘yan kwanaki kafin ya mutu ranar Alhamis.
Kunkurun, wanda ake gani a matsayin mafi tsufa a Afirka, ya zama wata dabba mai farin jini lokacin da Soun na ƙasar Ogbomosho mai ci, Oba Oladunni Oyewumi ya hau karagar mulki, inda basaraken ya dinga kula da kunkurun, da kula da lafiyarsa a lokacin da yake raye a doron ƙasa.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin ga jaridar Nigerian Tribune, Babban Sakataren Oba Oyewumi, Toyin Ajamu, ya jaddada cewa ba kawai mutanen Fadar ne za su yi kewar kunkurun sosai ba, wanda ya dinga jan hankalan mutane daban-daban a Najeriya da ƙasashen waje, amma duk wanda ya taɓa haɗuwa da Kunkuru Alagba a lokacin da yake raye.
A ta bakin Mista Ajamu: “Alagba ya kasance a Fadar tsawon ƙarni. Kunkurun ya riƙa karɓar baƙi ga sarakuna da dama a Ogbomosho a baya. Alagba ya shahara ne saboda Oba Oladunni Oyewumi, Soun na ƙasar Ogbomosho ya riƙa kula da shi da aljihunsa.
“Kunkurun yana da ma’aikatan fada guda biyu masu kula da shi. Su kan ba shi abinci, taimakon lafiya da sauran dabaru, don a tabbatar da cewa yana samun kula mafi kyau. Lokaci-lokaci, Kabiyesi ya kan yi raha da Algaba. A kullum kuma, masu yawon buɗe daga sassan duniya daban-daban su kan ziyarci Alagba. Iyalin fadar, al’ummar Ogbomosho da masu ruwa da tsaki suna cikin jimamin mutuwar Alagba”.
Sakataren Fadar ya bayyana cewa a halin yanzu ana shirye-shiryen ajiye gawar Alagba domin tarihi.