‘Yan Sanda A Kano Za Su Fara Tuƙa Baburan A Daidaita Sahu

206

Ƙungiyar Taimakon Kai-Da Kai ta ‘Yan Sanda ta Ƙasa wato Nigeria Police Multi-purpose Cooperative Society ta raba rancen Baburan A Daidaita Sahu 500 da babura 500 ga jami’an ‘yan sanda dake Shiyya ta 1 ta Kano.

Jaridar KANO FOCUS ta ruwaito cewa Shiyyar ta 1 ta haɗa Jihohin Kano, Jigawa da Katsina.

Babban Sakataren Ƙungiyar Taimakon Kai-Da-Kai ta ‘Yan Sandan ta Ƙasa, Dasuki Galadanchi ne ya raba rancen ranar Juma’a a Hedikwatar Shiyyar ta 1 dake Kano.

Mista Galadanchi, wanda Kwamishinan ‘Yan Sanda ne, ya ce tuƙa babura masu ƙafa uku yayinda jami’an ba sa kan aiki zai inganta jin daɗin rayuwarsu, ya kuma hana su karɓar cin hanci.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka karɓi babura za su biya N238,500 a cikin shekara huɗu da wata shida, yayinda waɗanda suka karɓi Baburan A Daidaita Sahu za su biya N735,000 a cikin shekara uku da wata shida.

A jawabinsa, Mataimakin Sifeto Janar na ‘Yan Sanda, Shiyya ta 1, Dan Bature, ya ce ana san ran tsarin bada rancen zai bunƙasa ƙwazon ‘yan sanda.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan