Yau Ake Bikin Bude Gasar Dr. Ahlan

191

Ranar wanka ba’a boyen cibi domin kuwa yau ake bikin bude gasar Ahlan wadda akayiwa lakabi da Ahlan Pre Season Tournament karo na 3.

Tun ajiya aka raba jaddawalin rukunin gasar.

Inda za a fara wasan farko tsakanin zakarun gasar wato kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Plateau United da misalin karfe 4:00 afilin wasa na Sani Abacha.

Ga tsaiwar jaddawalin rukunan kamar haka:

Rukunin A:

Katsina United
Jigawa Golden Stars
Lobi Stars
Abia Warriors
Nasarawa United

Rukunin B:

Kano Pillars
Plateau United
Rivers United
Yobe Desert Stars
Kada City

Rukunin C:

Wikki Tourists
Sokoto United
Kwara United
Pataskum Academy
Kano Selected

Rukunin D:

Rarara FC
Elkanemi Warriors
DMD
Enyimba International FC

Za ayi kwana tara ana yin wannan gasa inda za a kammalata ranar 15 ga watan Oktoba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan