Babu Adalci A Cikin Hukuncin Da Kotu Ta Yi Akan Zaɓen Abba Gida-Gida – Rabi’u Suleiman Bichi

111

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi ya bayyana cewa babu adalci a hukuncin da mai shari’a Halima Shamaki ta yi akan ƙarar da dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya shigar a gabanta
Rabi’u Sulaiman Bichi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
“Hakika Kotu Tayi Hukunci Irin Nata, Amma Mu A Gurinmu Wannan Hukuncin Bamu Ga Adalci A Cikinsa Ba. Kamar Yadda Alkaliya A Baya Tayi Mana Akan Karin Shaidu 8 (Zafafa 8), Ta Hana Mu Karo Su, Muka Daukaka Kara A Kotun Daukaka Kara (Appeal Court) Dake Kaduna, Muka Samu Nasara Har Zuwa Kotun Koli (Supreme Court)”
Ya ƙara da cewa “To A Yanzu Ma Haka Mun Daukaka Kara Kuma In Allah Ya Yarda Zamu Samu Nasara Kamar Yadda Mukayi A Baya”
“Duk Da Cewa Mun Samu Labarin Cewa Wadancan Makiyan Namu Kuma Makiyan Jihar Kano, Suna So Suyi Amfani Da Damar Su saka Rudani A Cikinmu. Suna ta yada Karairayi kamar yadda suka saba”
“To Muna Sanar Da Al’umma Cewa Mu Yan Kwankwasiyya Kanmu A Hade Yake, Muna Nan Zamuyi Iya Yinmu Don Ganin Mun Kwato Hakkin Al’ummar Jihar Kano”
A ƙarshe ya yi kira ga al’ummar jihar Kano musamman ƴan kwankwasiyya da su zauna lafiya.
“Muna Kira Ga Al’ummar Jihar Kano, Musamman Yan Jam’iyyar PDP Kwankwasiyya Da Su Zauna Lafiya, Su Zama Masu Bin Doka Da Oda Kamar Yadda Aka Sansu. Mu Cigaba Da Addu’a Allah ya Karbo Mana Hakkin Mu”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan