Gwamnatin Buhari Ta Jefa Al’ummar Ƙasar Nan Cikin Talauci Da Wahalar Rayuwa – Sheikh Gumi

459

Shararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya ce zaben 2019 shi ne zabe mafi muni a tarihin ƙasar nan, kasancewar a lokacin ne aka zabi gwamnatin da bata tsinanawa jama’a komi karkashin jagoranci Muhammadu Buhari.

Sheikh Gumi ya ɗora laifin wannan gwamnatin ne a kan manya-manyan ‘yan siyasan kudancin ƙasar nan, inda ya ce babu abinda gwamnatin Buhari ta yiwa al’ummar ƙasar nan in banda jefa su cikin talauci da wahalar rayuwa.


Malamin ya bayyana wannan abu a matsayin ganganci daga bangaren ‘yan siyansan kudancin ƙasar nan, in da ya ce sun marawa Buhari baya ne a zabukan 2015 da 2019 saboda wadansu buƙatu na kashin kansu.


Sheikh Gumi ya furta waɗannan kalaman na sa ne a lokacin da yake karbar bakuncin wani babban malamin addinin kirista, Isah El-Buba wanda ya ziyarcesa a gidansa dake Kaduna.


“Zaɓen shekarar 2019 shi ne zaɓen da yafi kowanne zaɓe muni da takaici a tarihin ƙasar nan, saboda zaɓe ne wanda ya raba kan al’ummar ƙasar nan a bisa jahilci da rashin sanin ya kamata”


“Bukatar mu ita ce mu samu shugaba wanda zai jagorance mu ba tare da nuna bambanci tsakanin wadansu bangarori ba, ina nufin wanda zai dauki dukkanin al’ummar ƙasara nan a matsayin ƴaƴansa”

“Sai dai kuma kash akasin hakan ne abinda muke fuskanta a yanzu. Kawunan sun rarrabu, ba kuma komi ya kawo wannan ba sai matsanancin talauci.


Duk miyagun laifukan da ake aikata a yanzu talauci ne ya kawo su. “Yan siyasa su ne masu kawo wa kasar nan matsala.

Wai gwamnatin dake ikirarin yaki da talauci ke nan, sai ga shi an gano daya daga cikin gwamnoninta yana cusa daloli cikin aljihu. Babu abinda zai bamu cigaban da muke bukata a kasar nan idan ba sahihin zabe ba.” Inji Gumi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan