Jami’a A Kano Za Ta Fara Koyar Da Darasin Likitanci

241

Farfesa Mustapa Isa, Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, ya ce Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, ta amince da karatun digiri na jami’ar na Darasin Haɗa Magunguna da Aikin Likita, wato MBBS.

Shugaban Jami’ar, wanda ya bayyana haka a maƙalar da jami’ar ta shirya don murnar Ranar Malamai ta Duniya ta 2019, ya ce za a fara karatun ne a shekarar karatu mai kamawa.

A cewar sa, an tanadi dukkan kayan aiki da ma’aikatan da suka wajaba da suka haɗa da Asibitin Koyarwa na Jami’ar don fara karatun.

“Kamar yadda ku ka sani, kafin ka tunkari Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa don bayyana buƙatarka ta fara wani kwas, dole ya zamana kana da wani shiri, kuma a matsayin shirin, kana buƙatar gine-gine, mutane da kayan aiki.

“Saboda haka, kafin mu je wajen NUC mu gabatar da buƙatarmu na kafa kwas ɗin MBBS, mun yi tsare-tsare da dama da suka haɗa da samo ma’aikata daga Kano da Arewacin Najeriya, kuma kamar yadda ku ka sani, wannan jami’a a cikin birni take, saboda haka, ana sha’awarmu sosai”, in ji Farfesa Isa.

Shugaban Jami’ar ya kuma bayyana cewa jami’ar ta yi sa’a da ta samu ma’aikata masu inganci da za ta fara kwas ɗin da su, waɗanda wasu daga cikinsu suna koyarwa a Arewacin Najeriya.

“Zan iya faɗa muku cewa rashin ma’aikata da aka bayyana a soshiyal midiya kwanan nan ba abu ne da ya dame mu ba. Tuni mun samu mutane waɗanda suka nuna sha’awar yin aiki da mu.

“Tuni ma mun ɗauki wasu ma’aikata aiki, kuma kamar yadda ku ka sani, muna da darussa a Tsangayar Darussan Likitanci na Tushe, kuma waɗansu daga cikin ma’aikatan nan sun cancanta su koyar a Kwalejin Nazarin Likitanci”, in ji Shugaban Jami’ar.

Ya ƙara da cewa tuni Gwamnatin Jihar Kano ta amince da mayar da Asibitin Ƙwararru na Abdullahi Wase dake Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta jihar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar.

Ya ce hikimar da ta sa aka zaɓi asibitin ya zama Asibitin Koyarwa shi ne don a tabbatar da nasarar shirin a cibiya da take mallakin Gwamnatin Jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan