Fim da Waƙa Halak ne Kuma Jihadi ne idan An bi Tsarin Musulunci Masu yi za su Samu Ɗumbin Lada Maras iyaka – Shek Moriki

248

Babban malami a hukumar Hizbah ta jihar Kano Sheikh Muhammad Tukur moriki Rijiyar Lemo ne ya bayyana haka cikin wani shirin mai suna Rabin Ilimi da ake gabatarwa a Mujallar Matashiya.

Malamin ya ce yin fim ko waƙa ya halatta kuma jihadi ne sannan kuma ana samun ɗimbin lada mai tarin yawa ga wanɗanda ke yin sana’ar tasu.

Malamin ya ƙara da cewa matuƙar an gina fim ɗin ko waƙar bisa tsari da koyarwar addinin musulunci to kuwa babu shakka masu yi na kwankwaɗar lada musamman idan suka aike da saƙo mai muhimmanci ga jama a.

Amma akasin hakan kuwa babu abinda zai haifar illa samun zunubi matuƙar ba a gina abin bisa koyarwa ta addinin musulunci ba.

Shek Moriki ya ce ko a zamanin Annabi S.A.W ma an yi waƙe wanda hakan ke nuni da cewa abin ya samo asali.

Amma yin bambaɗanci ko ƙarin gishiri a cikin waƙar haramun ne, inji shek Moriki.

Idan ba ku manta ba kuma a baya bayannnan ma mujallar Matashiya ta tattauna da shugaban hukumar tace fina finai da ɗab’i ta jihar kano Mallam Isma ila Na abba Afakallahu wanda ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu don ganin an tsaftace sana ar tare da karkaɗe bara gurbin ƴan masana antar.

Cikin tsarin da suke kuwa shi ne yin rijinta na kowanme fanni matuƙar mutum zai taka rawa a cikin sana ar hatta ɗan aike.


Rahoton Mujallar Matashiya

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan