Gwamnatin Jihar Kano Ta Ɗebi Malamai 600 Da Za Su Karantar Da Almajirai

183

Gwamnatin jihar Kano ta raba takardun kama aiki ga sabbin malamai guda 600 wanda zasu koyar da lissafi da turanci a wasu zaɓaɓɓun tsangayoyi guda 55 dake cikin fadin Jihar Kano.
Da yake jawabi akan lamarin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kano, Dakta Kabiru Shehu ya wakilta, ya ce shirin BESDA, shiri ne da yake samun tallafi daga bankin duniya wanda yake maida hankali akan ilmantar da yaran firamre, tare da rike su a makarantu, akan yanayin da yake sa yaran suke barin makarantun su da kuma dawo da karatun tsangaya ko na allo bisa turbar karatun zamani.
Dakta Kabiru Shehu ya kara da cewa wannan shirin na farko ne, kuma zai shafi makarantun tsangaya guda 55 da alarammomi 400.
Ya ƙara da cewa an nada kwamitoci guda biyu, in da dayan zaiyi aiki akan dawo da yaran da basa makaranta cikin makarantu, sa’annan daya kwamitin an dora masa alhakin tara jadawalin karatu da ya kamata a koyawa yara bayan lissafi da turanci, inji Shugaban ma’aikatan.
Har ila yau Dakta Kabiru Shehu yace gwamnati zata yi kwaskwarima ga dukkan makarantu da suke da matsalar rashin gyara a fadin Kano don samar da kyakkyawan yanayin karatu da koyarwa.
Daga karshe Dr. Shehu yace Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shirye ya le wajen kashe ko nawa ne domin tabbatar da dorewar samar da ingantaccen Ilimi a faɗin jihar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan