Ministan Wasanni Yashirya Yin Binciken Rashin Nasarar Super Falcons

171

Ministan Wasanni na kasarnan wato Sunday Dare ya bayyana cewar zaiyi bincike domin gamo musabbabin rashin nasarar da kungiyar kwallon kafan mata ta kasar nan tayi wayo Super Falcons.

Asakamakon rashin nasarar da Super Falcons din tayi yasa tagaza samun tikitin buga gasar motsa jiki daza ayi a birnin Tokyo na kasar Japan.

Awasan farko dai a birnin Abijan dake kasar Cote d’Ivoire antashi wasa 0 – 0 inda awasa na biyu anan Najeriya antashi 1 da 1.

Idan za a iya tunawa a kwanakin bayane dai mai horas da kungiyar kwallon kafan Matan ta Najeriya ya ajiye aikinsa wato Thomas Dennerby inda aka baiwa Danjuma inda kai tsaye ya kwace Captain daga hannun Desire Oparanozie ya damkawa Asisat Oshola.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan