Ina Fama Da Mura Sakamakon Aiki Tuƙuru Da Nake Yi- Buhari

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana fama da mura.
To, amma ya danganta murar tasa da yadda yake aiki tuƙuru a matsayinsa na Shugaban Ƙasa.

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da kasafin kuɗin 2020 a zauren Majalisar Dokoki ta Ƙasa a Abuja.

Bayan ya gama bin dukkan ƙa’idoji, kafin gabatar da bayan kasafin kuɗin filla-filla, ba tare da ɓata lokaci ba sai Shugaban Ƙasar ya nemi afuwa bisa rashin kyawun muryarsa.

Ya ce: “Kafin in karanto bayanan kasafin kuɗin filla-filla, zan nemi afuwa saboda rashin kyawun kyawun muryata.

“Kamar yadda za ku iya ji a muryata, ina fama da mura saboda ina aiki tuƙuru”.

Wannan magana ta jawo waɗanda ke cikin Zauren Majalisar da suka haɗa da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan; Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamia; ‘yan Majalisun Tarayya; gwamnonin jihohi; ‘yan Majalisar Zartarwa ta Ƙasa; da shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da sauransu suka ɓarke da dariya.

Kakakin Majalisar Wakilan, Femi Gbajabiamia, ya tausaya wa Shugaban Ƙasar bisa murar tasa.

“Shugaban Ƙasa, muna tausaya maka bisa murar da ka ke fama da ita”, Mista Gbajabiamia ya faɗa wa Shugaban Ƙasa haka yayin da yake gabatar da jawabinsa jim kaɗan bayan Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin 2020 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan