Tsoro Da Fargaba Ke Hana Ƴan Jarida A Ƙasar Nan Yin Binciken Ƙwaƙƙwafi – Halilu Getso

171

Fitaccen ɗan jaridar nan Alh Halilu Ahmad Getso, ya ce tsoro da fargaba ne ke hana yan jaridun kasar nan yin binciken kwakwaf a sha’anin aikin su na jarida.
Halilu Getso, Wanda yayi aiki da kafafen yaɗa labarai daban daban na ciki da wajen ƙasar nan, ya bayyana hakan ne Jim kadan da kammala taron karawa juna sani wanda tsangayar sadarwa ta Jamiar Bayero ta shirya kuma aka gudanar karkashin kulawar gidauniyar MacArthur.
Sannan kuma sai yayi kira ga yan jaridun kasar nan, da su cire kwadayi, kuma su daina nuna bangarenci na siyasa a binciken kwakwaf da suke yi.
Taron wanda ya gudana karkashin jagorancin Mal Ahmed Aminu, ya samu halartar Shugaban Jamiar Bayero, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, da Mal Aliyu Baba Barau da Malaman tsangayar sadarwa ta Jamiar Bayero, da Dan jaridar kasar Ghana Anas Armeyau Anas wanda ya gabatar da jawabi mai tsawo akan binciken kwakwaf a aikin na jarida, sai yan jaridu, dalibai da sauran alumma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan