Yadda Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin 2020

248

A ranar Talatar nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin 2020 da ya kai Naira Triliyan 10.729 a wani zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Da yake gabatar da kasafin kuɗin, Shugaba Buhari ya bayyana shi a matsayin Kasafin Kuɗin Cike Giɓi don ƙarfafa muhallin tattalin arziƙin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce kasafin kuɗin 2020 an gina shi ne a kan sabon Harajin VAT, yana mai ƙarawa da cewa za a yi amfani da ƙarin ne wajen samar da kuɗaɗe ga ilimi, lafiya da kayayyakin more rayuwa.

Za kuma a yi amfani da ƙarin da yake cikin kasafin kuɗin wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

Shugaban Ƙasar ya ce an gabatar da kasafin kuɗin ne a kan Dalar Amurka 57 kowace ganga, da kuma samar da ganga miliyan 1.86 kullum.

A cewar BBC Hausa, an ware wa ma’aikatu kuɗaɗe kamar haka:
Aiki da Gidaje – Biliyan N262
Sufuri – Biliyan N123
Hukumar Ilmi Matakin Farko ta UBEC – Biliyan N112
Tsaro – Biliyan N100
Aikin Gona – Biliyan N83
Albarkatun Ruwa – Biliyan N82
Ilimi – Biliyan N48
Lafiya – Biliyan N46
Hukumar Raya Arewa Maso Gabas – Biliyan N38
Birnin Tarayya – Biliyan N28
Neja Delta – Biliyan N24

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan