Ƙasar Ruwanda Ta Kafa Kamfanin Samar Da Wayar Hannu Na Farko A Afirka

132

A karon farko a nahiyar Afirka gwamnatin Ruwanda karkashin Shugaba Paul Kagame ta jagoranci kafa kamfanin samar da wayar hannu.
A ranar Litinin din nan aka yi bukin kaddamar da kamfanin mai suna “Mara da zai dinga samar da wayar hannu dake da Android a Kigali Babban Birnin Kasar.
Akwai kusan mutane 200 da za su yi aiki a kamfanin inda farashin wayoyin hannun da za su samar zai fara daga dala 129 zuwa 189.
A jawabin da Shugaban Kasar Ruwanda Paul Kagame ya yi a wajen ya fadi cewar za a iya sayen wayoyin ta hanyar biya a hankali a cikin shekaru 2 kuma ba wai ana sayen wayoyin hannu ne ba ne don burgewa ko nuna isa a sai don biyan bukatar yau da kullum kuma cikin hanzari.
Babban jami’in kamfanin Marsa mai suna Ashish Thakkar ya ce ba wai jojjona sassan wayar kawai za a yi a Ruwanda har ma da samar da dukkan kayan ta a kasar wanda wannan wani babban mafarkin nahiyar Afirka ne.
A Ruwanda dake son fitar da wayoyin zuwa kasashen Afirka kaso 52 na jama’a na samun yanar gizo.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan