Hukumar Samar Da Daidaito Wajen Rarraba Wutar Lantarki ta Ƙasa, NERC, ta sanar da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki guda takwas bisa aniyarta na soke lasisinsu nan da kwana 60 bayan sun ci bashin Naira Biliyan N30.1 a watan Yuli, 2019, kuma sun kasa biya.
A wata sanarwa da Dafe Akpeneye, Kwamishinan Shari’a, Bada Lasisi da Bin Doka ya sanya wa hannu kuma daka wallafa yau, NERC ta umarci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja, Benin, Enugu, Ikeja, Kano, Kaduna, Fatakwal da Yola su zo su yi bayanin abinda zai hana ba za a ƙwace lasisinsu ba a cikin wata biyu.
Hukumar ta ce Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarkin sun ƙi bin ƙa’ida ne ta hanyar ƙin dawo da kuɗaɗe.
“Kuɗaɗen da aka dawo da su zuwa Kamfanin Hada-hadar Wutar Lantarki na Ƙasa, NBET, sun nuna cewa Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarkin sun gaza biyan abinda ake sa ran su biya a watan Yuli, 2019”, in ji sanarwar.
NERC ta ce Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarkin guda takwas sun karɓi bashin Biliyan N36.1bn daga NBET na wutar da suka karɓa a watan Yulin 2019, sun dawo da Naira Biliyan N5.91 ne kaɗai, abinda ke wakiltar ƙwazon kashi 16 cikin ɗari. NERC za ta sa musu takunkumi ne bisa ragowar bashin Naira Biliyan N30.1
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan shi ne karon farko da NERC take aiwatar da wata doka mai suna Transitional Electricity Market Rule, dokar da ke tilasta Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki su biya kuɗin wuta ɗari bisa ɗari da sauran aikace-aikace. A yanzu NERC za ta doka gudumarta a kan Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki da barazanar soke lasisinsu a karon farko tun bayar cefanar da wutar lantarki a 2013.
Zuwa 1 ga Nuwamba, 2019, za a cika shekara shida da cefanar da wutar lantarkin, amma biyan kuɗin wuta da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki ke yi a cewar NBET ya yi ƙasa da kaso 30 cikin ɗari fiye da shekara uku da laifuka da dama, saboda ya kamata a ce samu Wasiƙar Lamuni ta Wata Uku daga NBET kowane lokaci daga yanzu.
Sakamakon abinda Kamfanin Tunkuɗo Wutar Lantarki na Ƙasa, TCN, ya siffanta da ‘rashin ɗa’a a kasuwar wutar lantarki’ da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki suka nuna, wanda ya munana a watan na Yuli, 2019, Sashin Kula da Kasuwanci na TCN, MO, ya dakatar da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki guda shida daga kasuwar hada-hadar wutar lantarki da suka haɗa da Kano, Ikeja, Fatakwal, Enugu a watan Agusta.
An dawo da su ne kawai bayan sun ƙara garanti na bankunansu, inda suka yi alƙawarin biyan kaso 100 cikin ɗari na aikace-aikacen da Sashin Kula da Kasuwanci na TCN, Sashin Kula da Kwamfutoci, NBET da NERC ke yi musu na aƙalla wata uku.
Amma kuɗin wutar da aka tura musu wanda ya kamata su biya ta hannun NBET sun wahala. NERC ta aika musu da mafi ƙarancin abinda ya kamata a ce kowane Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki yana biya, duba da rikicin kuɗi da suke ciki.
Amma, sun gaza biyan haka a bil ɗin watan Yuli, 2019.
Binciken ƙwaƙwaf na bashin kuɗin wuta na NBET na Yulin 2019 ya nuna cewa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Enugu ya fi kowane gazawa. NERC ya ce mafi ƙarancin abinda ya iya biya shi ne kaso 42 cikin ɗari daga bashin Naira Biliyan N4.112 da ake bin sa, amma Kamfanin Rarraba Wutar Lantarkin ya iya dawo da Naira Miliyan N400 ne kawai, abinda ke wakiltar kaso 10 cikin ɗari.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja zai dawo da kaso 45 cikin ɗari daga bashin Naira Biliyan N7.2, amma ya iya dawo da kaso 30 cikin ɗari ne kawai, wanda shi ne Naira Biliyan N2.152.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Benin ya gaza dawo da kaso 30 cikin ɗari na Naira Biliyan N4.37, ya dawo da Naira Miliyan N771.7 wanda ke wakiltar kaso 18 cikin ɗari.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Fatakwal shi ne na gaba a waɗanda suka gaza. Bai dawo da mafi ƙarancin kaso 21 cikin ɗari na Naira Biliyan N3.647 ba, ya iya biyan Naira Miliyan N383 ne ga NBET, wanda kaso 10 ne cikin ɗari.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano ya biya Naira Miliyan N800, kaso 24 cikin ɗari maimakon kaso 33 cikin ɗari na bashin Naira Biliyan N3.33.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna yana da bashin Naira Biliyan N3.834, amma ya biya Naira Miliyan N407.78 ne kawai, wanda kaso 11 ne cikin ɗari, maimakon abinda NERC ke buƙata na kaso 18 cikin ɗari.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ikeja zai biya kaso 49 cikin ɗari na bashin Naira Biliyan N7.4, amma ya biya kaso 40 ne kawai cikin ɗari, wanda shi ne Naira Biliyan N2.95.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Yola zai biya kaso 13 cikin ɗari na Naira Biliyan N1.95, amma ya biya Naira Miliyan 194.6 ne kawai, wanda kaso 10 ne cikin ɗari.
Hukumar ta ce gazawar Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarkin na biyan mafi ƙarancin bashin da ake bin su ya sa Ma’aikatar Samar Da Wutar Lantarki ta Najeriya, NESI, ta ce hakan yana yin barazana ga ɗorawar sauran ɓangarori, da kuma iya inganta samar wa masu amfani da wutar lantarki kyakkyawar wuta.