Mutane Miliyan 94 Ne Su Ke Fama Da Baƙin Talauci A Ƙasar Nan – Oxfam

Daraktan ƙungiyar Oxfam da ke bincike a ƙasar nan Mista Constant Tchoma ya sanar da cewar adadin mutane miliyan 94 ne su ke rayuwa a ƙasa da dala 2 a kowacce rana.
Tchona ya ce a watan Afrilu wannan adadi mutane miliyan 91 amma a cikin watanni 6 ya karu da mutane miliyan 3.
Ya ƙara da cewa idan ba’a ɗauki matakan da suka kamata ba nan da shekarar 2030 kaso 25 na jama’ar kasar nan za su kasance a yanayi na yunwa.
Duk da arzikin man fetur da gas da ƙasar nan take da shi amma cin hanci, rashawa da rikice-rikicen ta’adanci da na kabilanci sun hana kasar nan cigaba.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan