Home / Labarai / An Gano Birnin New York Mai Shekaru 5,000 A Ƙasar Isra’ila

An Gano Birnin New York Mai Shekaru 5,000 A Ƙasar Isra’ila

An gano abin da ya rage na tsohon birnin New York mai shekaru 5,000 a Isra’ila – birni mafi girma da tsufa a yankin.
Birnin a da na dauke da kusan mutum 6,000, akwai kuma hanyoyin bi da makwabta da wurin bauta.
Masu bincike da adana kayan tarihi sun bayyana cewa birnin da aka gano shi ne abu mafi girma a yankin.
Daraktocin da suka jagoranci hako garin sun bayyana cewa ”Wannan birni an kafa shi tun lokacin da ake amfani da tagulla a matsayin kudi; birni ne da dubban mutane masu al’ada daya suka zauna,”
”Ba shakka wannan wurin ya sauya bayan shekaru da dama.”
Wannan wuri da aka fi sani da En Esur, yana da girman eka 151, kusan ninki biyu idan aka kwatanta da abubuwan da aka gano a da.
Yadda taswirar garin yake ya hada da gidaje da wuraren shakatawa da hanyoyi kamar yadda hukumomi a Isra’ila suka bayyana.
An gano kananan abubuwa kusan miliyan hudu, da suka hada da kananan gumaka na duwatsu da aka kera su kamar mutum ko dabbobi wadanda akasarinsu daga Masar ne.
Konannun kasusuwan da aka gano a birnin sun tabbatar da yadda mutanen wurin a da suke sadaukar da dabbobinsu ga abubuwan bautarsu ta hanyar yanka ko kuma konawa.
Da alamu mutanen da suka zauna a garin sun zauna ne a wurin sakamakon akwai alamun ruwa da kasa mai kyau ta noma da hanyoyin da ‘yan kasuwa ke bi inda suke kasuwanci da ‘yan kasashe da dama.
Masu bincike da adana kayan tarihi sun dauki kusan shekaru biyu da rabi suna tona wurin da aka gano wannan gari.
Sun yi amfani da matasa kusan dubu 5,000 da suka taimaka.
Tun asali an fara tunanin cewa lallai akwai gari irin wannan a daidai wurin tun bayan da aka fara tona wurin domin gudanar da hanyar kwalta inda a nan ne aka fara ganin alamu.

Rahotan BBC Hausa

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *