Gasar Ahlan Pre Season Tournament da ake gudanarwa a jahar Kano naci gaba da daukan zafi inda wasu kungiyoyin kwallon kafan sun rasa maki inda wasu kuma sukeci gaba jan zarensu.
Domin kuwa kusan kowacce kungiyar kwallon kafa ta rasa maki inda ‘yan kadanne basuyi rashin nasara ba.
Domin kuwa hatta masu rike da kambun gasar sun rasa maki wato Kano Pillars awasan farko inda jiyama dakyar suka sha awasa na biyu.
Gasar dai ta bana za a iya cewa ba asan naci tuwona sai miya ta kare.
Ga jerin wasannin daza a buga yau:
Nasarawa United da Katsina United
Jigawa Golden Stars da Lobi Stars
El Kanemi Warriors da DMD
Abia Warriors da Rara F/C
Turawa Abokai