Jami’a A Taraba Ta Kori Ɗalibi Saboda Ya Soki Gwamna A Facebook

250

Jami’ar Jihar Taraba ta kori wani ɗalibi ɗan shekarar farko bayan ya yi ta sukar Gwamnan Jihar, Darius Ishaku a Facebook.

Jami’ar ta ce ta ɗauki wannan mataki na korar ɗalibin ne saboda ya gaza ‘kammala tsarin yin rijista’, wanda ya haɗa da sa hannu a fom ɗin rantsar da ɗalibai.

Joseph Israel, wanda ya samu gurbin karatu don ya karanta ‘Chemistry’, amma daga bisa ya canza kwas zuwa ‘Laboratory Science’, a makarantar da take mallakin Gwamnatin Jihar, an ƙwace takardar samu gurbin karatunsa a watan Satumba.

Wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 20 ga Satumba, 2019, da Mataimakin Magatakarda mai kula da Harkokin Karatu, Yakubu Fwa ya sanya wa hannu, ta zargi ɗalibin da kasa halartar taron rantsar da ɗalibai, da kuma ƙin cike fom ɗin shan rantsuwa.

“Ka sani cewa an janye takardar samun gurbin karatunka ne saboda gazawarka na kasa kammalawa tsarin yin rijista na Jami’ar Jihar Taraba, Jalingo, kamar yadda dokokin jamiar suka amince, abinda ya sa ka zama ɗalibi na bogi”, a cewar wasiƙar.

Amma, Mista Israel ya faɗa wa jaridar PREMIUM TIMES cewa wannan dalili da jami’ar ta bayar na ƙarya ne, kuma an yi amfani da shi ne don a hora ɗalibin da ya shahara da sukar gwamnan a Intanet.

Ya musanta cewa bai halarci taron rantsar da ɗalibai ba, ya ce kuma ya sa hannu a fom ɗin shan rantsuwa.

“Kuskuren da na yi shi ne ban yi hoto ba a ranar. Ni ba mutum ne da ya damu da hoto ba. Amma, ina da mutum sama da 20, waɗanda za su iya shida cewa ina wajen tare da su a wannan rana. Na kuma sa hannu a fom ɗin da aka ba mu”, in ji shi.

Takardar korar ba ta kawo dokokin jami’ar da suka ce a kori ɗalibin da ya ki halartar taron rantsar da ɗalibai ba.

Daraktan Yaɗa Labarai na Jami’ar, Sanusi Saad, ya faɗa wa PREMIUM TIMES a waya cewa yana sane da al’amarin, amma ba shi da iko da isasshen bayanin da zai iya yin tsokaci a kai.

Ya ce Shugaban Jami’ar ba ya nan balle ya yi ƙarfin bayani.

Takardu da PREMIUM TIMES ta ci karo da su sun nuna cewa Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta taɓa ba Mista Israel sammace zuwa gaban wani Kwamitin Hana Maguɗin Jarrabawa, da zargin rashin ɗa’a da kurakurai a karatu.

Wannan ɗalibi ya bayyana a gaban wannan kwamiti ranar 15 ga Yuli, 2019 kamar yadda aka umarce shi.

Mista Israel ya ce kwamitin ya fuskance shi bisa yadda yake zargin gwamnan, ya tambaye su ko akwai wata doka da ta hana ɗalibi yin amfani da soshiyal midiya don bayyana ra’ayinsa bisa yadda ake shugabanci a jihar.

Ya ce kwamitin, wanda bai bada wata amsa ba, ya umarci da ya tafi har sai an kammala bincike.

“Da wannan zalunci da aka yi, abin baƙin ciki ne a yi tsammanin cewa a yanzu Jihar Taraba na fuskantar munafunci mafi girma da ƙulle-ƙulle a tsakanin ma’aikatan gwamnati da malaman jami’a waɗanda sun kunyata ilimi”, in ji Jen Jibrin, wani ɗan rajin kare haƙƙin bil Adama mazaunin Jalingo.

Mista Israel ya yi amfani da shafinsa na Facebook wajen yin caccaka bisa tsarin shugabancin Mista Ishaku.

A ranar 26 ga Afrilu, ya wallafa: “Da a ce Gwamna Darius zai siyar da motoci bakwai daga cikin tawagar motocinsa kaɗai, da ya warware matsalolin Jami’ar Jihar Taraba.

“Gwamna Darius mutum ne da aka gwada shi, kuma ya gaza, kwana 100 na kowace gwamnati suna nuna alƙiblar wannan gwamnati, gwamnatin Darius ba ta da alƙibla, gwamnatinsa ita ce mafi muni a shekaru 28 da ƙirƙirar Jihar Taraba”, ya rubuta haka.

Ya ƙara rubuta: “Ina kira ga dukkan waɗanda fatansu ya yi sama da su ajiye fatansu har 2023, wataƙila za mu samu gwamna mai hangen nesa kuma mai yi da gaske”.

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan