Majalisar Dattijai Za Ta Rage Yawan Jam’iyyun Siyasar Najeriya

46

Majalisar Dattijai ta Ƙasa ta ce za ta rage yawan jam’iyyun siyasar dake shiga zaɓe a ƙasar nan daga 91 zuwa biyar ta hanyar yin doka.

Majalisar Dattijan ta bayyana haka ne ranar Laraba a yayin wani taron ganawa da shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC bisa jagorancin Shugabanta, Farfesa Mahmoud Yakubu.

Majalisar ta bayyana rashin gamsuwa bisa yawan jam’iyyun siyasar da suka tsayar da ‘yan takara a zaɓukan gwamna da za a yi a Jihohin Kogi da Bayelsa.

Yayinda yake jawabi a taron ganawar, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ya ce yawan ‘yan takarar da suke yin takara a zaɓen ya saɓa da Dokar Zaɓe da aka yi wa kwaskwarima.

Ya ce a bisa Dokar Zaɓe, jam’iyyun siyasa, waɗanda suka kasa cin kujera ko ɗaya a manyan zaɓukan da suka gabata, za a soke rijistarsu.

A ɓangarensa, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai na INEC, Sanata Kabiru Gaya ya ce: “Jam’iyyun da ba su taɓuka komai ba bai kamata a sa su a kan takardar zaɓe ba.

“Dokar zaɓe da ake aiki da ita yanzu ta hana jam’iyyun da ba su taɓuka komai ba a zaɓukan da suka gabata shiga zaɓe. Akwai buƙatar mu gyara dokar mu rage yawan jam’iyyun siyasar zuwa biyar.

“Wannan kwamiti a shirye yake wajen rage yawan jam’iyyun siyasa don alkinta kuɗaɗen masu biyan haraji”.

Da yake mayar da jawabi, Shugaban na INEC, ya ce ji ta shiga ruɗu wajen ɗaukar matakin rage yawan jam’iyyun siyasa, sakamakon wasu ƙararraki da ake kan sauraro, waɗanda za su iya canza hukuncinta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan