Nasarata Ta Arewa Maso Yammace Gabadaya Inji Malikawa

177

Biyo bayan zaben da akayi a Rivers na mukamin da shugaban marubuta labarin wasanni na jahar Kano ya samu wato Lurwanu Idris Malikawa Garu ya bayyana cewar wannan nasara tasa ta Arewa maso yamma ce gabadaya.

Malikawa dai ya kwashe shekaru da dama a fannin aikin jarida da jagorancin shugaban marubuta labarin wasanni na jahar Kano inda ahedu da dama ta bangaren ayyukansa ansami nasarori da dama.

A zaben da aka gudanar dai shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa yakoma kujerarsa babu hamayya inda akazabi Mayoyo matsayin sabon mataimakin shugaban inda kuma Babafemi aka zabeshi amatsayin mataimakin sakatare.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan