NBAIS Ta Saki Sakamakon Jarrabawar Ɗalibai ta 2019

197

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantun Koyon Larabci da na Ilimin Addinin Musulunci ta Ƙasa, NBAIS, ta sanar da cewa ɗalibai 28,645 ne suka samu nasara daga cikin ɗalibai 36,239 da suka zauna Jarrabawar Kammala Manyan Makarantun Nazarin Larabci da Ilimin Addinin Musulunci, SAISSCE ta Watan Yuni/Yuli ta 2019.

A lokacin da yake sanar da sakamakon a Kaduna, Magatakardar Hukumar, Farfesa Mohammed Shafi’u Abdullahi ya bayyana cewa ɗaliban sun zauna a manyan darussa da suka haɗa da Larabci, Turanci, Nazarin Addinin Musulunci, Lissafi, Ilimin Sanin Halittu, Chemistry da Physics.

A ta bakinsa, “Ɗalibai 28,645 daga jimillar ɗaliban da suka zana jarrabawar sun cinye dukkan darussansu. Waɗanda suka faɗi a wasu darussa ba ma ganin su a matsayin waɗanda suka faɗi, saboda su ma sun ci wasu darussan, abinda ke nufin za su iya ci gaba da karatunsu da credits biyar”.

A wani ci gaban na daban, dattijo kuma tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Farfesa Ango Abdullahi, ya roƙi hukumar da ta haɗa makarantun allo da na gwamnati don magance matsalar yara da ba sa zuwa makaranta.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan