Shin Ko Abdullahi Abbas Zai Iya Zama Sarkin Kano?

158

Ta yiwu Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya gaji Sarautar Kano bayan da Gwamma Abdullahi Umar Ganduje ya kira da ‘mai jiran gado’.

A cewar jaridar Kano Focus, da ma dai ana kiran Mista Abbas da Ɗan Sarki Jikan Sarki, kasancewarsa jikan Gidan Dabo.

Gwamna Ganduje ya kira Mista Abbas da ‘mai jiran gado’ ne ranar Laraba a wata walimar da aka shirya don murnar samun nasarar da gwamnan ya samu a kotu.

Wannan magana ta gwamnan ta sa an fara ce-ce-ku-ce cewa gwamnan yana son Mista Abbas ya gaji Sarkin Kano mai ci.

Mista Abbas ɗa ne ga Galadiman Kano, Abbas Sanusi, kuma jikan Sarki Muhammad Sanusi I.

A kwanan nan ne wata ƙungiya da ba ta gwamnati ba mai suna The Renaissance Coalition ta yi zargin cewa gwamnan yana kitsa tumɓuke rawanin Sarki Muhammad Sanusi II mai ci, wanda ɗan kawun Mista Abbas ne.

Amma dai gwamnan ya musanta zargin.

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi dai sun daɗe suna takun sakamakon bambance-bambancen siyasa.

Gwamnan ya ƙirƙiri sabbin masarautu huɗu da sarakuna, wani yanayi da masu sharhi suke ganin ya raunana Masarautar Kano da mulkin Sarki Sanusi.

Amma dai gwamnan ya sha nanata cewa an ƙirƙiro masarautun ne don kawo gwamnati kusa da jama’a.

A sakamakon haka, akwai ƙararraki da ke gaban kotuna daban-daban a Kano waɗanda Masarauyar Kano da masu naɗa Sarki suka shigar, inda suke ƙalubalantar matakin gwamnan na ƙirƙirar sabbin masarautu.

Gwamna da farko, sannan sarki

Da yake mayar da martani ga jawabin gwamnan, Umaru Kashe- Kobo, wani mai goyon bayan Mista Abbas, ya ce sun fassara sanarwar a matsayin amincewa da buƙatun shugabansu guda biyu.

“Gwamnan ya bayyana goyon bayansa kuma ya nuna soyayya ta gaskiya ga shugabanmu.

“Muna fata wannan zai share hanya ga Ɗan Sarki ya gaji gwamna a 2023, sannan ya cika gurin dukkan ‘ya’yan Sarki ta hanyar zama Sarkin Kano”, in ji shi.

To, amma Mista Kashe-Kobo, wanda Shugaban Jam’iyyar APC ne na Ƙaramar Hukumar Gwale, ya musanta duk wata jita-jita da ke nuna cewa maganar tana nufin tumɓuke rawanin Sarki mai ci.

“Ba kuma kuskure ba ne don gwamnan ya faɗi sunan wanda zai gaje shi.

“Za ku iya tunawa cewa shi ma Malam Ibrahim Shekarau ya zaɓi Salihu Takai a matsayin wanda zai gaje shi, amma wannan bai hana jam’iyyar yin zaɓukan fitar da gwani ba.

“Saboda haka, muna fatan gwamnan zai umarci dukkan magoya bayansa su zaɓi shugabanmu a 2023”, ya ƙara da haka.

Annoba ko rashin nasara

A gargajiyance, Sarautar Kano a buɗe ta ke ga dukkan ‘ya’yan tsatson Dabo ba tare da ware wani ba a matsayin ‘mai jiran gado’.

Waɗanda aka samu guda uku sun yi sarauta ta haka sun ƙare ne ko dai a annoba ko rashin sa’a.

Kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, Sarkin Musulmi ya naɗa Galadima Tukur don ya gaji mahaifinsa, Sarki Muhammadu Bello, wani yunƙuri da ya haifar da yaƙin basasar Kano.

A Jamhoriya ta Biyu, Gwamna Abubakar Rimi ya yi wa Ɗan Buran Abubakar alƙawarin kujerar, amma ya kasa cikawa.

Haka kuma, Shugaban Ƙasa na Mulkin Soja, Janar Sani Abacha an ce ya yi wa Wambai Abbas Sanusi, mahaifin Mista Abbas alƙawarin kujerar, amma ya rasu kafin ya aiwatar da shirin nasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan