Ronaldo Yaci Kwallo Ta 700 Atarihi Akan Luxemburg

200

Dan wasan kasar Portugal wato Christiano Ronaldo ya jefa kwallonsa ta 700 atarihi awasan da kasar Portugal ta fafata da Luxemburg adaren jiya inda suka casa Luxemburg din daci 3 da nema.

Wannan kwallon daya jefa itace kwallo ta 94 dayajefawa a kasarsa ta haihuwa wato Portugal inda ya kusa ya tarar da dan wasan kasar Iran daya jefa kwallaye 109 ga kasarsa wato Ali Daei.

Ali na kasar Iran yace babu shakka sai Ronaldo ya karya tarihin daya kafa.

Shikuma Jose Mourinho ya bayyana cewar Ronaldo yana da shekaru 34 amma shine ja gaba abin bai bashi mamaki ba tunda koda yaushe tunaninsa shine yaya za ayi ya sami nasara.

Ronaldo ya jefa kwallaye 5 a Sporting Lisbon ya jefa kwallaye 118 Manchester United ya jefa 451 a Real Madrid yanzu kuma ya jefa kwallaye 32 a Juventus ga kuma kwallayen daya jefa a Portugal.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan