Kome Wasan Najeriya Da Brazil Yake Nuni Bayan Antashi 1 Da 1?

209

Kasar Brazil da Najeriya sun tashi wasa kunnen doki wato 1 da 1 wasan da aka fafata shi a kasar Singapore.

Najeriya ne suka fara jefa kwallo kafin atafi hutun rabin lokaci ta hannun dan wasa Joe Aribo, bayan kuma andawo daga hutun rabin lokaci ne Brazil suka rama kwallonsu ta hannun dan wasa Casemiro.

Tun bayan da aka kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika dai Najeriya wasannin sada zumunta guda 2 ta fafata inda duka kunnen doki suka buga wato wasan da suka kara da Ukraine inda suka tashi 2 da 2 sai kuma wasan yau dasuka fafata da Brazil wato 1 da 1.

Ita kuwa a bangaren kasar Brazil tun bayan da suka lashe gasar Copa America sun fafata wasannin sada zumunta guda 4 inda basuyi nasara ako wasa dayaba, awasan da suka kara da Columbia antashi 2 da 2, sai wasan da suka kara da Peru inda Brazil sukai rashin nasara daci 1 da nema, haka atsakiyar makonnan sun fafata da kasar Senegal suntashi 1 da 1 da kuma wasan da suka kara da Najeriya ayau inda shima aka tashi 1 da 1.

Wannan wasa na yau kamar yana nuni da cewa kasar Najeriya tana da matasan ‘yan wasa kuma zasu iya tunkarar kowacce kasa a duniya domin ga misali nan awasan da Brazil ta fafata da Najeriya ayau inda akayi kare jini biri jini.

A jaddawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar na watan Satumbar daya gabata na tsaiwar kowacce kasa a duniya Najeriya tazo mataki na 34 da maki 1482 inda kuma Brazil tazo matsayi na 3 da maki 1719.

Alamu sun nuna cewa Najeriya tauraruwarsu zata haska sosai anan gaba ganin yadda suka sami matasan ‘yan wasa masu kwazo da hazaka.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan