Bayan Allah Bani Da Wanda Yafi Goodluck Jonathan A Rayuwata – Gwamnan Jihar Bauchi

325

Wasu kalamai da gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya yi sun bar baya da ƙura. Mutane dai na ta tafka muhawara akan kalaman na gwamna, gwamnan dai yayi kalaman ne jiya a jihar Bayelsa, bayan da aka zaɓe shi a matsayin shugaban yakin neman sake zaban Gwamnan jihar Beyelsa Diri Douye a zaben da za a fafata a jihar.

Lokacin da gwamnan yake jawabi sai yace: “….Tsohon shugaban ƙasa (Jonathan) mai gidana ne……., sannan bayan Allah, bani da wani sai Good Luck Jonathan”.

Jama’a na ta muhawara akan ma’anar hakan, magoya bayansa sunce yana nufin a siyasance ne, wasu kuma sun ce “kawai yayi saɓo, ya fito ya nemi gafarar Allah.”

Tun bayan kalaman dai babu wani makusancin ga gwamnan daya fito ya fadi hakikanin abinda gwamnan yake nufi.

Turawa Abokai

3 Sako

 1. Assalamu’alaikum.
  Don Allah jama’ar Nigeria Ku my kara hakuri, mu daina la’antar shuwagabanni,domin zagin su illane garemu Baku daya.
  Son zagin su kan iya kawo Karin gushewar tunanin su har gagara yi mana abinda Muke fata a yankunanmu.
  Na code.
  Daga,
  Alamin Muhammed Gadagau
  ( A.M.G)
  Sairan waka.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan