Gwamnan Jihar Kebbi Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 30 Domin Gina Coci-Coci

115

Rahotanni daga jihar Kebbi sun bayyana cewa Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu ya bayar da gudumuwar naira miliyan 30 ga al’umman kirista dake masarautar Zuru domin gina cocina.


Shugaban Ƙungiyar Kiristocin na ƙasa (CAN) Rev James Manga ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai. Ya ce gudumuwar za ta taimaki al’ummar kirista a yankin masarautar Zuru wajen gina coci da sauran ayyuka.


Manga ya ce wannan ne karo na farko da al’umman kirista ta samu makuden kuɗaɗe daga gwamnan jihar ta Kebbi.


Ya ce baya ga gudumuwar naira miliyan 30, Gwamna Bagudu ya kuma ziyarci al’ummar kirista a lokacin kirsimetin da ta gabata domin taya su murna.


Ya ƙara da cewa gwamnan har ila yau ya bada gudumuwar buhunan shinkafa da tufafi da sauran kayayyakin abinci zuwa ga cocina a fadin jihar a bikin kirsimati da ya gabata.


A ƙarshe ya yi kira ga gwamnan da ya tabbatar da cewa ya shigar da kiristoci cikin majalisarsa, domin a shekaru huɗu da suka gabata gwamnan bai saka kirista ba a ƙunshin majalisarsa. Wanda hakan babban ƙalubale ne da kiristoci ke fuskanta a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan