Home / Labarai / Mutane Huɗu Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Gini A Jihar Lagos

Mutane Huɗu Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Gini A Jihar Lagos

Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa ta ce mutane 4 ne suka mutu wasu 6 kuma suka jikkata a sanadiyyar ruftawar gini a jihar Legas.
Femi Oke-Osanyintolu, janar manajan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ya shedawa kafafen yada labarai cewa, al’amarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata a sakamakon mamakon ruwan sama da aka sheka a yankin.
Ya ce wata mace da ‘yayanta uku sun mutu a sanadiyyar ruftawar ginin sai dai mijin matar ya tsira da ransa.
Oke-Osanyintolu ya ce, ginin dake kan tudu ne ya rufto kan wani gida dake kasa, sai dai a cewarsa ba’a tabbatar da adadin mutanen da birabizan ginin ya danne ba, amma masu aikin ceto suna cigaba da gudanar da ayyukansu.
Wani kwararre a yankin ya ce, ana yawan samun matsalolin ruftawar gini a fadin ƙasar nan sakamakon yadda wasu masu tsara gine gine basa mutunta dokokin da suka shafi aikin tsara gine ginen.
A mafi yawan lokuta, ana jibga abubuwa masu nauyin gaske a saman ginin, kuma a wasu lokutan ana amfani da kayayyakin gini marasa inganci.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *