Akwai buƙatar gwamnatin jiha da rundunar ƴansanda na Kano da subi sahun takwarorin su na Jihar Katsina, wajen gudanar da bincike game da yadda ake gudanar da Gidajen Mari a Jihar Kano.
Faya-fayen bidiyo dake zagawa a zaurukan sada zumunta game da yadda Hukumar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bankado wani Gidan Mari a garin Daura abu ne mai matukar tada hankali.
Daruruwan yara da aka taskance a dan karamin gida mai dakuna shidda sun tsinci kawunan su cikin rayuwa mai cike da hadarin gaske domin baya ga cututtuka dake da nasaba da cunkoso da rashin tsafta, yaran sun fuskanci matsalar tashi samun abinci mai gina jiki.
Sai kuma batun zarge-zargen cin zarafi da yaran suka ce ana musu, musamman ma zargin yin lalata (luwadi) da suka ce wasu daga cikin malaman su nayi dasu.
Haka na akwai zargin musgunawa wadda har takai wasu daga cikin su sun samu colon tabin kwakwalwa (hauka). Kenan idan muka duba al’amarin duka za’a fahimci cewar sharrin dake tattare da irin wadannan gidaje yafi alkhairin dake tattare dasu.
WANENE MAI LAIFI?
Ni a irin tawa fahimtar gwamnatocin mu da suka bari are gudanar da irin wadannan gidaje su ke da laifi, domin kuwa kamata yayi ace masu irin wadannan gidaje Sun samu sahalewar gwamnatin tun kafin su fara wannan harka. Haka nan yakamata ace kafin a ba mutum dama sai ya samu lasisi tukuna ta hanyar gabatar da wata shaida dake nuna irin horo da mutum ke da shi wajen Kula da kangararrun yara.
Wani karin sakaci kuma shine ko dai na rashin hukumomi dake da alhakin kula da wadannan gidaje ko kuma na sakacin da irin wadannan hukumomi or nunawa wajen bibiyar yadda ake gudanar da irin wadannan gidaje.
Haka na akasarin gwamnatocin jihohi a Najeriya basu dauko batun gyaran tarbiyya da muhimmanci ba, shi yasa a yanzu haka, makarantun da muke dasu na gyaran tarbiyya basu taka kara sun karya ba. Hakan yasa dole al’umma su dogara da irin wadannan gidaje da ake gudanarwa cikin yanayi mai munin gaske.
A yanzu dai abinda ya rage shine my jira muga yadda gwamnatocin jihohi dama hukumomin ‘Yansanda na musamman jihohin arena inda are da irin wadannan gidaje zasu dauki matakan bincika da kuma rushe wannan tsari na Gidan Mari baki daya. Ina kyautata tsammani abinda aka bankado a Gidan Marin Mallam Bello dake Daura na iya zama hoto da zai nuna mana halin da irin wadannan matasa ke ciki a irin wadannan gidaje.
Masu iya magana dai sunce “ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanda.”
Kawu Sule Rano
Malami Ne A Sashen Nazarian Halayyar Dan Adam Na Jami’ar Bayero Da Ke Kano